Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kira kasar Masar ta daina cin zarafin 'yan rajin kare hakin bil Adam


Shugaban Masar Abdel Fattah el-Sissi
Shugaban Masar Abdel Fattah el-Sissi

A jiya Laraba ne Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice da kungiyoyin rajin kare ‘yanci suka yi kira ga kasar Masar, da ta dakatar da cin zarafin masu rajin kare ‘yancin bil Adama, da kuma daina yi musu katsalandan a ayyukansu.

Kungiyoyin kasa da kasa na kare hakkin dana dam guda 14, cikinsu har da kungiyar Human right Watch da Amnesty International, suka ce, ya kamata jami’an Masar su dakatar da tambayoyin da suke yi wa masu rajin kare hakkin bil Adama, da kuma hana su yin tafiye tafiye da kokarin

Cikin wata sanarwa da hadakar kungiyoyin suka fitar, wadda ke cewa “yakamata hukumomi su daina cin zarafin kungiyoyin su kuma dakatar da binciken da suke musu, wanda ke barazanar daurin shekaru 25 a gidan kaso ga masu fafutukar kare hakkin bil’adama”.

Kungiyoyin sun dade suna zargin ma’aikatan tsaron Masar, da daure mutane ba bisa ka’ida ba. Mataimakin Shugaban Amnesty mai kula da shirye-shiryen Gabas ta Tsakiya da Amurka ta Arewa, Said Boumedouha ma cewa yayi, “Misira na yiwa masu fafutukar kallon makiya kasar maimakon hada kai da su don ciyar da Masar gaba.

A makon da ya gabata ne sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka, John Kerry, yace akwai matsalar karuwar dakile masu rajin kare ‘yancin bil’adama a Masar cikin ‘yan watannin nan.

XS
SM
MD
LG