Wani Bam Ya Halaka Jami’an Tsaro Uku A Mogadishu

Shugaban rundanar ‘yan sandan Mogadishu, Ali Hersi Barre, ya ce ana tsare da matukin motar wanda ya samu munanan raunuka

‘Yan sanda a Somalia sun ce wani bam da aka dasa a cikin wata mota kusa da wani kantin shan shayi da ke daura da ofishin ‘yan sanda a Mogadishu, ya halaka jami’an tsaro uku bayan da ya tashi.

Shugaban rundanar ‘yan sandan Mogadishu, Ali Hersi Barre, ya ce ana tsare da matukin motar wanda ya samu munanan raunuka yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da bincike.

Wannan hari da aka kai yau Laraba, na zuwa ne bayan wanda aka kai ranar Litinin a birnin Beledwyene, wanda ya jikkata akalla mutane shida ciki har da dakarun wanzar da zaman lafiya na Kungiyar tarayya Afrika.

A wata hira da ya yi da sashen Somalia na Muryar Amurka, shugaban ‘yan sandan Beledwyene Kanar Ali Dhuh Abdi, ya ce harin ya auku ne a filin tashin jirage, kuma jami’an tsaro sun yi nasarar dakile wani hari na biyu.

Ya kara da cewa an kai harin ne ta hanyar yin amfani da na’urar computer kirar tafi-da-gidanka.

Yanzu haka hukumomin tsaro sun ce suna tsare da mutane 20 da ake zargi na da hanun a wannan hari.