Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Tarayyar Turai sun cimma yarjejeniya da Turkiya a kan bakin haure


Firayim Ministan Turkiya Ahmet Davutoglu yana jawabi a karshen taron kasarsa da Tarayyar Turai yau Talata, Maris 8, 2016
Firayim Ministan Turkiya Ahmet Davutoglu yana jawabi a karshen taron kasarsa da Tarayyar Turai yau Talata, Maris 8, 2016

Shugabannin turai na kasashe 28 sun cimma yarjejeniya da Turkiya ta wucin gadi akan bakin haure har zuwa ranar 17 da ake kyautata zao zasu cimma matsyi na dindindin a taron kolinsu

Shugabanin kungiyar tarayyar Turai sun fada yau Talata cewa, da alamun sun cimma yarjejeniya ta wucin gadi da hukumomin kasar Turkiyya dake Ankara, kan tasa keyar dubban 'yan gudun hijira zuwa Turkiyya, kuma sun ce suna da kwarin guiwar cewa za'a cimma cikakkiyar yarjejeniya a lokacin wani taron koli da za'a yi makon gobe.

Bayan watanni da wakilan kungiyar mai kasashe 28 suka yi suna bayyana rashin fahimtar juna da cacar baki, shugabannin suka ce sun amince zasu baiwa Turkiyya karin kudi domin ta taimakawa 'yan gudun hijira, sannan zata sassauta bada visa ga 'yan kasar Turkiyya, kuma zata gaggauta batun shigar Turkiyyar cikin kunigyar tarayyar turan, sannan a gefe daya kuma ita Turkiyya zata taimaka wajen hana korarar bakin haure zuwa Turai.

Shugaban Faransa Francois Hollande, yace taron kolin da suka yi "ya haifar da fatar zasu iya magance batun 'yan gudun hijira ta wajen hadin kai tsakanin kasashen Turai, da kuma inganta hanyoyin hada kai da Turkiyya."

Yanzu an zura ido zuwa 17 ga wata, lokacinda kungiyar zata gudanar da taron koli inda za'a kammala aiki kan yarjejeniyar.

XS
SM
MD
LG