A muhawarar da aka yi a birnin Flint da ke Jihar Michigan, ‘yan takarar biyu na jam’iyyar Democrat, sun sha ban-ban da na jam’iyyar Republican wandanda suka fi maida hankali wajen sukar junansu.
A lokacin da ya ke jawabi, Sanders ya ce irin halayen da ‘yan takarar Republican ke nunawa, alama ce da ke nuna cewa idan har ya zama shugaban kasa, gwamnatinsa za ta bunkasa fannin kula da lafiyar kwakwalwa.
Birnin na Flint mai yawan mutane dubu 100 wadanda akasarinsu bakaken fata ne kuma suna rayuwa ta kunci, ya sha fama da matsalar gurbataccen ruwan sha.
Sanders wanda shi ya fara jawabi a muhawarar, ya bayyana alhininsa kan yadda ya ga iyalai ciki har da yara suke fama da matsalar gurbataccen ruwan sha.
Ita kuwa Clinton kira ta yi ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su fitar da kudade domin a shawo kan matsalar.