Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan rikicin Syria, Staffan de Mistura ya isa birnin Geneva a yau Laraba, a wani shiri na komawa kan teburin tattaunawa da bangarorin da ke yaki a kasar ta Syria.
Sai dai lura da cewa har yanzu ana sa ran sauran wakilai su isa birnin, mai yiwuwa a samu tsaiko na ‘yan kwanaki wajen komawa kan teburin tattaunawar.
Mai magana da yawun de Mistura, Jesse Chahine, ta ce wasu daga cikin wakilan ba za su samu halartar taron ba har sai zuwa ranar lahadi ko kuma Litinin.
Kuma Majalisar ta Dinkin Duniya ta daura alhakin wannan tsaiko akan wasu shirye-shirye da ya kamata a yi gabanin taron.
A wata sanarwa da aka aikawa Muryar Amurka, gamayyar ‘yan adawar na kasar ta Syria ta ce ba lallai ba ne su halarci tarukan farko.
Itama gwamnatin Syria ta nuna alamun cewa ba za ta halarci taron ba sai daga baya, wanda hakan ke nuna alamun cewa zaman tattaunawar ba zai kankama ba har sai na da zuwa ranar 14 ga watan nan na Maris.