Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu A Najeriya


Shugaba Jacob Zuma.
Shugaba Jacob Zuma.

Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya fara ziyarar aiki a Najeriya, inda zai gana da shugaba Muhammadu Buhari domin tattauna abubuwa na difilomasiya da cinikayya.

Har ma da yadda kasashen biyu zasu yi mu’amula da juna domin tallafawa sha’anin noma da hakko ma’adanai, da kuma daukar matakan da zai kai ga karin samun nasarar yaki da ta’addanci da Najeriya ke fuskanta.

Kakakin shugaban Najeriya, Mallam Garba Shehu, yayi karin bayani kan muhimmancin wannan ziyara. Inda yace kasashen biyu na da abubuwa a gaban su, duk da yake Afirka ta Kudu tayi fice a bangaren tattalin arziki, musamman wajen noma da hakar ma’adanai. Duk da yake gwamnatin Najeriya na ganin dogaro da Man fetur ya zama hadari, hakan yasa ta koma bangaren Noma da hakar ma’adanai. Kan wannan bututuwa ne shugabannin zasu tattauna.

Kasar Afirka ta Kudu na da manyan manyan kamfanoni dake kasuwanci a Najeriya, hakan yasa za a duba hanyar bude harkokin kasuwancin da yan Najeriya zasu ci moriya. Haka kuma Najeriya na neman taimakon Afirka ta Kudu, wajen fara kera makamai a gida.

Domin Karin Bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG