Buhari Ya Cika Alkawari Bayan Shekaru 30

Kaftin din ‘yan wasan Golden Eaglets Nduka Ugbade, wadanda suka kafa tarihi a shekarar 1985, lokaci da suka lashe kofin kwallon kafa ta duniya na ‘yan kasa da shekaru 17, yanzu kam suna cikin farin ciki.

Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya yi masu alkawari a wacen lokaci amma juyin mulkin da akayi yasa ba’a cika masu alkawarin ba yanzu Allah ya bada ikon cika alkawarin.

Ugbade yace jiya kawai sai ga sako akan wayarsa ta hannu daga banki cewa kudade sun shiga ajiyarsa ta banki.

Ugbade yana mai cewa a madadin shi da sauran ‘yan wasan suna godiya ga shugaba Muhammadu Buhari, Ministan Matasa da wasani Solomon Dalung da Amaju Pinnick shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta Najeriya a bisa wannan cika alkawari na Gwamnatin Najeriya.

‘Yan kungiyar flying Eagles da suka ci gasar nahiyar Afirka sun sami Naira 500,000, ‘Yan Golden Eaglets da suka lashe gasar bara a kasar Chile sun sami Naira miliyan daya da dubu dari biyu.