Wani sabon binciken jin ra’ayi a Amurka ya nuna cewa galibin ‘yan kasar na goyon bayan gwamnatin kasar a kokarin da ta ke yi na hurawa babban kamfanin nan na Apple wuta don neman hanyar duba bayannan sirrin wayar daya daga cikin maharan garin San Bernadino da ke jihar California, wanda ya faru cikin shekarar da ta gabata.
Binciken jin ra’ayin na kwanan nan da cibiyar Pew ta yi akan mutane fiye da 1,000 ya gano cewa mutane kashi 51 na goyon bayan gwamnatin Amurka akan kamfanin Apple ya yarda ya bude wayar da Syed Rizwan Farook ya yi amfani da ita, yayinda kashi 38 din mutanen su ka ce bai kamata kamfanin ya bude wayar ba saboda hakan zai bada kafar ganin bayannan wasu masu amfani da wayar. Kashi 11 na mutanen kuma basu bayyana ra’ayinsu ba.
A halin da ake ciki kuma, wani mai shari’a da ke kare wasu daga cikin iyalai 14 da Farook, wani musulmi haifaffen Amurka, tare da matarsa ‘yar kasar Pakistan Tashfeen Malik suka kashe 'yayansu, ya ce zai rubata wata wasika ta goyan bayan alkalin da ya ba kamfanin Apple umurnin bude wata hanyar samun bayanan wayar Faruk.
Kamfanin Apple na cigaba da yin jayayya da wannan umurnin, shugaban kamfanin Tim Cook ya fadawa masu amfani da wayar jiya litinin cewa bukatar gwamnatin Amurka na da nauyi sosai.
A wata wasika zuga dumbin masu amfani da wayar, Mr. Cook ya ce kamfanin na fasaha ba ya tausayawa ‘yan ta’adda. Amma, idan har kamfanin Apple ya amince da bukatar gwamnatin Amurka ta bude bayanan wayar Farook, to lallai kam hakan zai bude hanyar samun bayanna wasu masu amfani da wayar nan gaba.
Ya kara da cewa yin hakan zai sa a ga bayannan banki ko na kudi, da na asibitin masu amfani da wayar har ma da wurin da su ke, da kuma hotunan da suke dauka, babu kuma wani mai hankali da zai so a yi mashi haka a cewar Mr. Cook.