Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Shekarar 2026 Za'a Samar Da Sabuwar Kasar China


Wasu garuruwa 12, a kasar China, nada komai da kasani, akwai hanyoyi masu kyau, ruwan sha, kasuwanni na zamani, manya-manyan gine-gine na zamani, wajajen shakatawa, kasuwa, asibiti, makarantu, da dai duk wani abu da aka sani garin da yafi kowane gari a duniya yana da shi. Amma a cikin wadannan garuruwan babu abu daya, shine Mutane!

Kasar China, sun fara wani aiki na samar da wasu garuruwa da suke da bukatar idan Allah ya kai rai da lafiya, shekarar 2026, zasu kwashe mutane da suka kai yawan milliyan 250, ‘yan kasar don su sama musu matsugunni. Kasar ta China suna daga cikin kasashe da su kafi yawan mutane a duniya.

Bugu da kari tattalin arzikin kasar China, na daya daga cikin mafi karfi a fadin duniya. Wannan wani tsari ne da babu wata kasa da ta tabayin a duniya. Mafi akasarin gari na farawa da daidaikun mutane,sannu a hankali mazauna garin kan kokarta wajen raya garin. Amma wannan wani sabon tsari irin na kasar China , don magance matsalar muhalli ga ‘yan kasar nada matukar muhimanci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG