Za'a Yiwa Cutar Sha'inna Diran Mikiya a Najeriya.

Shugaba Buhari da Bill Gate da Aliko Dangote

Shugaba Buhari da Bill Gate da Aliko Dangote

Gwamnonin jihohin Sokoto da Yobe da Borno da Kaduna ne suka hadu a kaduna domin rattaba hannu kan yarjejeniyar da zata tallafawa shirye shiryen rigakafin.

A wannan makon ne attajirin nan kuma shugaban kamfanin Microsoft, Bill Gates ya hada kai da gwamnonin jihohin Najeriya 4 da hamshakin mai kudin Afirka, domin karfafa hanyar da za’a kawar da cutar shan’inna da kuma fadada rigakafi ga kananan yara a Arewacin Najeriya.

Gwamnonin jihohin Sokoto da Yobe da Borno da Kaduna ne suka hadu a kaduna domin rattaba hannu kan yarjejeniyar da zata tallafawa shirye shiryen rigakafin.

An dai yi yarjejeniyar ne tsakanin Gidauniyar Bill & Melinda Gates, da kuma gidauniyar ‘Dangote har ma da jakadan Amurka zuwa Najeriya.

Haka suma jihar Kano da Bauchi zata zasu sabunta yarjejeniyar su da wannan kungiyoyin. Dalilin wannan yarjejeniya dai shine gidauniyar Bill da Dangoten su raba hannu wajen biyan kudaden da za’ayi amfani wajen gudanar da shirye shiryen. Wanda zasu taimakawa jihohi wajen baiwa yara rigakafin cutar kyanda dake haifar da shan’inna, domin kawar da cutar da kashi 80 cikin 100 kafin karshen shekara ta 2018.