Daga nan sai ya bukaci ‘yan gudun hijirar su kwantar da hankular su.Ga abinda yake shaida musu.
‘’Yanzun abin da gwamnati keson yi muku shine ta gina muku gidaje sabbi, idan kun koma zaku je ku zauna a ciki ne, da yawan ku da aka kone muku gidaje yakamata gwamnati ta gina muku wasu gidaje ne’’
Sai dai kuma a waje daya gwamnatin jihar ta mayar da martini game da wannan sukan da hukumar kare hakkindan adam din take yi mata na rashin kulawa da ‘yan gudun hijirar.
Mr Anthony Dan Buran dai shine kwamishinan yada labarai na jihar Taraban ga kuma abinda yake cewa.
‘’Kokawan nan da suka yi basu kyautata muna ba, duk abin nan da muke bayar suce sun koka, to sun koka kamar yaya? Ko kunji cewa gwamnatin tarayya ta baiwa jihar Taraba gudun mowa ne abasu bata basu ba? Ya kamata idan ana sara to a rika duba bakin gatari, domin mu muna bakin kokarin mu a matsayin mu na gwamnati muna taimaka musu, muma muna rokon gwamnatin tarayya tazo ta dubi yanayin da wadannan mutanen suke ciki, su dan kara taimako akan wanda jihar Taraba take yi wa wadannan mutanen’’
Kawo yanzu dai dubban ‘yan gudun hijira ne ke warwatse a ciki da wajen jihar kamar yadda wakilin sashenHausa na VOA Ibrahim Abdul Azeez yace ya gane wa idanun sa, a garin Bantaje.
Ga Ibrahim Abdul AZeez din da ci gaban bayani