Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Fadakar Da Matasa Dabarun Kaucewa Fadawa Tarkon 'Yan Ta'adda


Amurka tana horas da matasa Musulmi da Kiristoci domin lakantar hanyoyin tantance sahihancin labarai da aka wallafa a kafafen sada zumunta.

A jamhuriyar Nijar wakilai daga kasashe 8 na yankin sahel na halartar wani taron horos wa akan ma’amala da yanar gizo wanda aka yiwa lakabi da TECH CAMP wanda kasar Amurka, ta shirya da hadin guiwar majalisar matasan kasar Nijar domin fadakar da matasan yankin dabarun kaucewa fadawa tarkon masu aika miyagun sakwanni a shafukan sada zumunta.

Lura da yadda rubuce rubucen ‘yan ta’adda ke mamaye shafuka sada zumunta wanda kuma ke matukar tasiri a kawunan matasan Afirka, masamman nay akin Sahel masu fama da matsalar ta’addanci yasa kasar Amurka shirya horaswa na TECH CAMP wanda zai ba matasa Musulmi da Kiristoci damar lakantar hanyoyin tantance sahihancin dukkan wasu labaran da aka wallafa a kafafen sada zumunta.

Alhaji Idi Bara’u , jami’in, hulda da ‘yan jarida a ofishin jakadancin Amurka a Nijar, yace wannan zai bada dama ga matasa sun fahimci cewa akwai sako na gina kasa akwai sako na ci gaba akwai sako na zaman lafiya da ake iya samarwa ko isarwa ta hanyar yanar gizo akasin yadda kungiyoyin ‘yan ta’adda kamar Boko Haram, keyi amfani da manhajojin whatsapp da Twitter.

A cikin kwararrun da aka gayyato daga kasar Amurka cikin su harda Jamila Fagge, ta muryar Amurka, tace abin da yake faruwa shine su ‘yan ta’addan suna amfani da da wadannan fannonin fiye da yadda Gwamnati ke amfani, ita Gwamnati kawai ta dauka har yanzu lokcin da ne sai sun ga damar bayyana ra’ayin su zasu bayyana, kafin su bayyana ra’ayinsu har wani ya riga ya samu wadannan matasan , kuma kowa ya san yadda suke da yunwar samu labarai da bayanai, to idan har Gwamnati taga cewa haka ya faru kafin taje wajan su sun riga sun dauki abun da suka dauka, dole ne ya zamo cewa idan har Gwamnati tana son ta cimma burinta wajen shawo kan ‘yan ta’adda ya zamo sune masu bayyana ra’ayinsu kafin sun ‘yan ta’addan su bayyana ra’ayinsu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG