Kuma an samu gagarumin nasra ga wannan sabo da ita gwamnatin wannankasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa tace zata bada gudun mowa wajen yaki da taaddanci a Najeriya.
Kasar tace zata tura tawagar ta domin taje taga sassan arewa maso gabas na Najeriya inda aka raba mutane da muhallin su aka rusa musu masallatai da coci-cocin su da gadoji da asibitoci da makarantu suga irin abinda shin me mutane suke so ayi musu.
Wannan sune kalaman mai baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawara a harkokin yada labarai Garba Shehu. Lokacin da suke tattaunawa da Umar Faruk Musa
Da kuma Umar din ya tambaye shi bai ganin cewa zaifi kyau a kammala yaki da ‘yan boko haram din tukunna,shine sai ya fara bayani kamar haka.
‘A to ai dama maganar biyu ce,yakin nan koda an gama shi, tsugunno bata kare ba musali shugaba Muhammadu Buhari yana maganar cewa akwai mutum yafi miliyan 2 wadan da basu da muhalli, wadanda yawancin su mata ne da yara, kuma kashi 70 cikin miliyan 2 din nan mata ne da yara.
Kana kashi 70 yara ne da basu san muhallin sub a kuma ma basu san iyayen sub a, sabo da haka ana bukatar gagarumin taimako, irin su ciyarwa, gina muhalli da sauran su.
Sai kuma ansa hannu akan yarjejeniya da yawa, musammam guda 6 da akayi, wadda a cikin su, akwai wadda ta bada damar Najeriya ta biyo hakkin ta na kudaden da aka sace a Najeriya.
Akwai yarjejeniyar cewa idan Najeriya ta nuna cewa wadannan kudaden mallakin ta ne gwamnatin kasar ta Dubai zata taimaka domin a dawo dasu.
Ga Umar Faruk Musa daci gaban tattaunawar