Tsohon sarkin garin Alhaji Abbas Ibrahim Sambo, ya rasu ne a kasar Makka a lokacin tureninyar da ta yi sandaiyar mutuwar daruruwan mutane a aikin hajjin bana.
A yammacin yau litinin ne gwamnatin ta fitar da sanarwa tareda umurtar wazirin garin Mr. Linus Ibrahim da ya rike ragamar mulkin garin har zuwa lokacin da za a nada sabon sarki.
“Mutanen Zing su yi hakuri su jira su ga sakamakon matakin da gwamnati za ta dauka, a yi hakuri da duk abinda gwamnati ta ce.” In Ji Sylvanus Giwa, mai taimakawa gwamna a fannin manema labarai.
Dokar dai ta fara aiki ne daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe.
Shima Wazirin garin, Mr Sylvanus Ibrahim ya yi wannan kira, “a kwantar da hankali, tun da gwamnati ta ce ga wanda zai yi riko kafin hankali ya kwanta, kafin kuma a samu wanda zai rike mu a wannan masaurata baki daya.”
Tuni dai aka tura karin ‘yan sanda har da ma sojoji domin kwantar da tarzoma a wannan gari.
Ga karin bayani a rahoton Ibrahim Abdulaziz:
Your browser doesn’t support HTML5