Kimanin mutane dubu sittin ke mutuwa kowace shekara sakamakon kamuwa da cutar Zangaye, mai nasaba da cizon kare wanda galibi kananan yara, ne dan haka ne Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar 28, na Satumban kowace shekara domin ta zama ranar yaki da cutar.
Malam Isiyaku Salihu,darakta na ma’aikatar kare lafiyar dabbobi a jahar Maradi ya ce “Ciwon Zangaye ciwo ne wanda mafi wawanci ake samu daga karnuka wanda idan kare ya ciji mutun ko kuma wata dabba ya ke iya samata Zangaye, sai ka ga mutun yana wata hauka kamar yadda kare ya keyi shi yasa ake ce masa Zangaye wannan kuma yana iya kawo wa har ga mutuwa a duniya gaba daya yake kashe kimanin mutane 60,000, saboda ciwo ne wanda karnuka ne wandanda suke a sake.”
Gwamnatin kasar Nijar, tayi shelar dukkan wani mai Kare ya kai shi domin ayi masa alura kyauta a wani mataki na riga kafi saboda ita cutar zangaye akwai ta da matukar ila kuma ga tsadar magani .
Kwamishina kiwon lafiyan dabbobi na jahar Maradi, Malam Isiyaku Salihu, ya kara da cewa idan Kare ya ciji mutun yana iya daukan kwanaki ashirin ko arba’in kafi cutar ta bayyana, saboda haka ya umarci jama’a dasu yi amfani da wannan dama na yi wa kawunan su riga kafi.
Ya ce idan har aka yiwa Karnuka aluran riga kafi bazasu kamu da cutar Zangaye ba balle har su ciji wani su sa masa cutar zangaye.