An Fara Binciken Faduwar Jirgin Saman Sojojin Najeriya Yau A Kaduna

Jiragen saman sojojin Indiya, samfurin Dornier 228 irin wanda ya fadi a Kaduna.

Jami'ai na ayyukan agaji sun ce dukkan mutane 8 dake cikin wannan jirgin na horaswa na sojoji sun mutu a bayan da ya fado a kusa da makarantar sojoji ta Kaduna

Babban hafsan sojojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar, ya kafa wani kwamiti na musamman da zai binciko musabbabin faduwar wani jirgin saman mayakan Najeriya samfurin Dornier-228 yau asabar a Kaduna.

Jirgin ya fado kan wani gida yau da safe a barikin Ribadu, ya kashe dukkan mutane 8 dake cikinsa.

Babu wani mutum a kasa da ya mutu a sanadin wannan lamarin.

Wata sanarwar da darektan yada labarai na rundunar mayakan saman Najeriya, Air Commodore Dele Alonge, ya bayar ta ce wannan kwamitin bincike zai kasance karkashin jagorancin wani mai mukamin Air Vice Marshal.

Yace shi kansa babban hafsan mayakan saman Najeriya, Air Marshall Abubakar, ya soke rangadin da yake shirin kaiwa fatakwal, kuma zai ziyraci inda wannan lamarin ya faru tare da jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa.

Jami'in yace jirgin ya tashi ne da misalin karfe 6:45 na safiya a kan hanyar zuwa Abuja.

Wakilinmu Isa Lawal Ikara ya tattauna da jami'an ayyukan agaji da kuma wani wanda ya ganewa idanunsa wannan hatsarin, ya aiko da wannan rahoto...

Your browser doesn’t support HTML5

Jirgin Saman Soja Ya Fadi Yau Asabar A Kaduna - 3'04"