Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya ta Bada Sanarwan Nadin Sabbin Mukamai


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

Gwamnatin tarayya ta bada sanarwan nadin sabbin mukamai da suka hada shugaban hukumar Kwastan,daSakataren gwamnatin tarayya, sai kuma babban jamii a fadar shugaban kasa, da shugaban hukumar shige da fice,Sauran mukaman dai sune, masu taimaka wa shugaban kasa akan harkokin majilisu kasa guda biyu wato na dattijai dana wakilai.

Wadanda aka nada din ko sune Injiniya Babachir David Lawal a matsayin sakataren gwamnatin tarayya, Alhaji Abba Kyari, Babban jamii a fadar shugaban kasa,Shugaban hukumar Kwastan na kasa Hammed Ibrahim Ali, Shugaban shige da fice na kasa Mr.Kure martin Abeshi, sai Sanata Ita S.J Babban mai taimaka wa shugaban kasa akan harkokin majilisar Dattijai, sai kuma Hon.Suleman A. Kawu Babban mai taimakawa shugaban kasa akan harkokin majilisar wakilai.

Wannan nadin dai ya fara aiki ne nan take a yau din nan 27 ga watan agusta.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG