ZABEN2015: Kashi 76 Na Masu Rijista Sun Karbi PVC - inji INEC

Wani dan Najeriya yake kada kuri'arsa a zaben fidda 'yan takara.

Jihar Zamfara ce take kan gaba a karbar katunan Zabensu Na Din-din-din.

Hukumar zabe ta Najeriya tace kusan kashi 76% cikin dari na mutane da suka yi rijista a kasar sun karbi katunan zabensu na din din din.

Jihar Zamfara ce take kan gaba inda kusan kashi 97% cikin dari na wadanda suka yi rijista a jihar sun karbi katunan zabensu.

Hajiya Amina Zakari, daya daga cikin kamishinonin hukumar zaben, wacce ta zanta da wakilin Sashen Hausa Umar Farouk Musa, tace samun nasarar kara rarraba katunan zaben, yana daga cikin fa'idojin da aka samu na dage zaben, domin sun sami karin lokaci wajen baiwa mutane katunansu.

Hajiya Amina, tace cikin dalilan nasaroin shine kara zuwa kusa da jama'a a unguwannninsu, maimakon tsayawa a kananan hukumomi, inda watakil hakan yake da wahala ga wadansu.

Hajiya Amina tace jihar Gombe ce ta biyu, a yawan karbar katunan zabensu, jihar Ogun ce take a zaman ta karshe.

Ga dalilai data bayar.

Your browser doesn’t support HTML5

Raba katin zabe na din din din.