Kakakin majalisar dokokin Jihar Kebbi, Aminu Musa Jega, ya bada sanarwar cewa shi da sauran shugabannin majalisar sun yi murabus daga kan mukamansu. Yace a yanzu dai, zasu ci gaba da kasancewa a jam'iyyar PDP, amma kuma ba su san abinda zai kasance nan gaba ba.
'Yan sa'o'i kadan bayan da ya bada sanarwar murabus din ne kuma, sai wasu 'yan majalisar suka yi zama cikin dare suka ce sun tsige shi, sun kuma nada Hassan Muhammad Shalla a zaman sabon kakaki.
A Jamhuriyar Nijar, hukumomi sun jefa tsohon magajin garin birnin Maradi, Kassoum Moukhtar a gidan kurkuku. Babu bayani na abubuwan da suka sa aka daure shi, amma wasu mukarrabansa sun ce ba zai rasa nasaba da zarge-zargen da ake yi masa na handama da zarmiya ba.
Wasu 'yan gudun hijira daga arewa maso gabashin Najeriya, cikinsu har da wasu 'yan Gwoza, sun yi zanga-zanga a Abuja domin kira ga gwamnati ta mike ta kwato musu garuruwansu daga hannun 'yan ta'adda. Wani daga cikinsu ma ya bayyana yadda ya shafe kwanaki 6 kan dutse da yadda suka ga ana bi gida-gida ana yanka mutane, ciki har da limamin Gwoza.
A Jos, hukumomin Jami'ar Jos sun kafa kwamitin da zai bi diddigin zanga-zangar da dalibai suka yi cikin wannan makon har ta kai ga rufe jami'ar na sai illa ma sha Allahu.
Your browser doesn’t support HTML5