Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kakakin Majalisar Jihar Taraba Yayi Murabus


Tsohon kakakin majalisar jihar Taraba
Tsohon kakakin majalisar jihar Taraba

A yau litinin, kakakin majalisar dokokin jihar Taraba, Josiah Sabo Kente, ya yi murabus,biyo bayan wani sabon rikicin siyasa daya sake kunno kai a jihar ta Taraba. Kuma tuni har aka nada Hon. Mark Hussaini, a matsayin sabon kakakin majalisar, ta jihar Taraba.

Tsdohon kakakin, Josiah Sabo Kente, yana da alaka ta kurkusa da tsohon mukaddashin gwamnan jihar, Alhaji Garba Umar, wanda Kotun Kolin ta kasar dake Abuja, ta cire a makon jiya, sannan ta ba da umarnin nada Alhaji Danladi, a matsayin sabon Gwamnan jihar.

Jihar Taraba dai ta fada cikin rikicin siyasa tun lokacin da tsohon Gwamnan jihar, Danbaba Suntai, ya kwanta rashin lafiya bayan hatsarin jirgin sama.

Kakakin Majalisar Taraba - 3"26"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

XS
SM
MD
LG