WASHINGTON, DC —
Akalla Sojoji biyar ne suka mutu a Mubi dake arewa maso gabshin Najeriya, sakamakon fashewar wani bom a gefen hanya, da ake kyautata cewar 'yan bindioga masdu tada kayar baya ne suka dasa.
Lamarin ya faru ne a mararaban Mubi, a lokacin da ake fafatawa tsakanin 'yan Boko Haram da Sojojin Najeriya, dake samun tallafi daga Maharba da kuma 'yan Kato da Gora, a cikin Maharban mutun daya ya rasa ransa, wasu hudu kuma na samun magani a asibiti.
Sakataren Maharban Mista Philips James, yace wannan abun da ya faru bai razana su ba ko kadan, kuma zasu ci gaba da sagewa wuri ganin cewa sun samu galaba.