Cristiano Ronaldo Da Lionel Messi: Wanene Cikinsu Ya Fi Tabukawa Kasarsa A Filin Kwallo?

Cristiano Ronaldo na Portugal da Lionel Messi na Argentina

‘Yan wasan tamaula biyu da suka fi suna a duniya, Lionel Messi da Cristiano Ronaldo, zasu sake karawa da juna yau talata a wasan sada zumuncin da Portugal da Argentina zasu yi a filin wasa na Old Trafford, watau na ‘yan Manchester United a Ingila.

Ronaldo zai shiga wannan filin wasa na Manchester United, inda ya taba yin yayi a zaman shahararren dan wasa lokacin yana shekara goma sha wani abu, yayin da shi kuma Messi zai bayyana a gaban magoya bayan United wadanda ya bakanta musu rai a 2009 da 2011 lokacin da ya cire kungiyarsu daga wasan lashe kofin zakarun kulob na Turai.

Amma wanene gwani daga cikin wadannan gwanaye biyu?

A karawar karshe da kasashensu biyu suka yi a 2011 dai Messi shi ne ya samu galaba. Messi ya jefa bugun fenariti cikin raga, Argentina ta doke Portugal da ci 2-1, a bayan da shi Ronaldo ya jefa ma Portugal kwallonta daya tilo.

Dukkansu biyu sun jefa kwallaye a raga ma kasashensu a wasannin kasa da kasa na karshe da suka bhuga. A ranar larabar da ta shige, Messi ya jefa kwallo daya a lokacin da Argentina ta doke Croatia da ci 2-1 a London. Shi ma Ronaldo ya jefa kwallo kwaya daya da kasarsa Portugal ta samu ta doke Armenia a wata gasar Turai ranar jumma’a.

Daga cikin ‘yan wasan nan biyu, wanene kuke ganin ya fi tabuka ma kasarsa wani abu?