Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nahiyar Turai na Barazanar Ficewa Daga FIFA


Shugaban Kasar Rasha da Shugaban FIFA
Shugaban Kasar Rasha da Shugaban FIFA

Dan wasan gaba na Kasar, Brazil, Henrique, yayi nasaran cin kwallaye 3, a wasan da kungiyar sa ta Brisbane, ta kasar Austerlia, ta buga da Newcastle, wace tunda aka fara kasar Lik, ba’a saka mata kwallo ko daya a raga ba.

Henrique, dai ya shiga wasan ne a lokacin da Jean Carlos, ya ji ciwon kafin hutun rabin lokaci, yaci kwallayen, a mintoci 49, 72 da kuma 89, a cikin wasan.

A wani labarin kuma Shugaban hukumar Lik, din kwallon kafar , ta kasar Jamus, Reinhard Rauball, yace, hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, tana shawaran fita daga cikin kungiyar FIFA, idan har FIFA, bata wallafa, duk abun wani Lauya dan kasar Amurka, Michael Garcia, ya bayana ba, dangane da karban bakunci gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya na shekaran 2018 da 2022.

Rauball, ya furta haka ne bayan da wani Alkali, a kasar, Jamus, ya wanke kasashen Rasha da Qatar, abinsa zargin cin hancin da rashawar dangane daukar bakuncin gasar ta cin kofin duniya, da za’a yi a wadannan kasashen.

Gasar Cin Kofin Duniya -1'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:04 0:00

XS
SM
MD
LG