Koch din Najeriya Stephen Keshi, na saka ido kan neman samun nasara a wasan da Najeriyar zata buga da Bafana Bafana kungiyar kwallon kafar Afirka ta Kudu. Kuma ya bayyana cewa a wasan da sukayi da Kongo na share fagen shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekara ta 2015 nada matukar wahala.
Keshi dai yace, babu wata kungiya da take kanwar lasa ce a duk nahiyar Afirkan, alokacin da Super Eagles suka lashe wasan su 2-0 dakuma fatan ganin sun sami guri a gasar ta 2015.
Wasan kwallon kafa ya canza, al’umma na kara girma, dole muma mu kara girma kuma muci gaba dayin duk abin da mukeyi na ganin mun kara kwazo da karfi, inji Keshi alokacin dayake magana da goal.com
Ya kara da cewa, babu laifi wasan mu da mukayi da Kasar Kongo, gaba dayan mu munyi wasan mai kyau kuma ina ganin da munci karin kwallaye a bayan dawowa kashi biyu na wasan.
Najeriyar dai zata rike bakuncin Bafana Bafana na Afirka ta Kudu ranar larabar nan, kuma tana bukatar cinye wasan na karshe rukunin ta na Group A.