An nada Xi Jinping a zaman sabon jagoran China

Sabbin shugabannin kasar China a lokacin da ake gabatar da su yau alhamis a Babban Zauren Taron Al'umma a Beijing

An gabatarwa da duniya sabbin shugabannin kasar China a Babban Zauren Taron Al'umma na Beijing
An nada Xi Jinping a zaman sabon jagoran kasar China, inda ya karbi mukamin sakatare janar na Jam’iyyar Kwaminis mai mulkin kasar, kuma shugaban majalisar sojanta mai karfin iko.

Mataimakin shugaba Xi, wanda aka jima ana sa ran zai karbi ragamar jagorancin jam’iyyar daga hannun shugaba Hu Jintao mai barin gado, yana kan gaba a cikin jerin sabbin shugabannin kasar su shida da aka bayyanawa duniya yau alhamis a lokacin da suka jeru a kan dandali a Babban Dakin taron Al’umma na Beijing.

Mutanen sune zasu zamo wakilan Babban Kwamitin Siyasa, majalisar zartaswa mafi karfi a kasar China. Sauran wakilan wannan majalisar mulki su ne firimiya mai jiran gado Li Keqiang, da masanin tattalin arzikin da yayi karatu a kasar Koriya ta Arewa, Zhang Dejiang, da babban jami’in farfaganda Liu Yunshan, da mataimakin firimiya Wang Qishan, da shugaban jam’iyyar Kwaminis na Shanghai Yu Zengsheng da kuma shugaban jam’iyyar na Tanjian, Zhang Gaoli.

Xi, wanda zai karbi mukamin shugaban kasa a watan Maris, ya fadawa ‘yan jarida yau alhamis cewa sabbin shugabannin su na fuskantar babban nauyi, amma zasu mike tsaye don inganta rayuwar mutane miliyan dubu daya da dari uku na kasar China.