Kasar Rasha da kuma China sun hau kujerar naki a kan wani kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da zai kakabawa Siriya takunkumin da ba na soja ba, yayinda Amurka ta kuduri aniyar daukar wani mataki na dabam na matsawa gwamnatin shugaba Bashar al-Assad lamba.
Kudurin da aka takawa birki dama yana niyar kara wa’adin aikin manzon Majalisar Dinkin Duniya na musamman Kofi Annan da kwanaki 45, da zai hada da masu aikin sa ido a Siriya 300. Membobin kwamitin sulhun suna tunanin kada kuri’a kan kudurin da zai kara wa’adin da kwana 30.
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya tace Kwamitin Sulun ya “gaza” a kan batun Siriya, saboda haka yanzu Amurka zata yi aiki tare da abokan kawancenta ba karkashin inuwar Kwamitin Sulhun ba, wajen tunkarar gwamnatin Assad.
An tsaida wannan shawarar ne yayinda ake ci gaba da gwabza fada tsakanin ‘yan tawayen Siriya da dakarun gwamnati a babban birnin, kwana daya bayan harin bom da ya kashe ministan tsaron kasar da kuma wadansu jami’an gwamnati biyu lokacin suna wani taro da ya kunshi manyan kusoshin gwamnati.