Hillary Clinton ta ziyarci Afirka a wannan satin a daidai lokacin da kasuwancin China a Nahiyar da kuma hannun jarin da ta ke sakawa ke ta habbaka.
Masu nazarin al’amura sun ce daya daga cikin manyan dalilan ziyarar Sakatariyar Harkokin Wajen na Amurka zuwa Afirka, shi ne ta tabbatar cewa ba a bar Amurka a baya ba, a gasar da ake kan cinakayya da kuma ikon fada a ji.
China ta zarce Amurka a 2009 a zama babbar abokiyar kusuwancin Afirka, kuma adadin wannan harka ta kasuwanci sai dada gaba-gaba ya ke yi.
Bangarorin biyu sun yi kasuwancin dala miliyan dubu 160 bara, idan aka kwatanta da na dala miliyan dubu 10 cikin tsawon shekaru 10 da su ka gabata, da kuma na dala miliyan dubu a tsawon shekaru 20 kafin nan.
Hakazalika tallafin da China ke bai wa Afirka da kuma jarin da ta ke sakawa ya yi matukar karuwa, saboda China na sa ran mai da wannan Nahiya mai dinbin ma’adanai, wurin samar da abubuwan sarrafawa a masana’antunta da ke ta habbaka.
Jami’an gwamnatin China sun bayar da sanarwa a watan jiya cewa kamfanonin China kimanin 2,000 ne ke hada-hada a Afirka, da jarin da ya kai wajen sama da dala miliyan dubu 14, wanda wannan kari ne na kashi 60 cikin dari cikin shekaru 2.
Firimiyan China Hu Jintao ya yaba da irin wannan huldar a wani taron da aka yi kwanan nan da manyan jami’an gwamnatoci daga kasashe fiye da 50 na Afirka a birnin Beijing, ciki har da Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma, da Shugaban Cote d’Ivore Alassane Dramane Ouattara da kuma Firayim Ministan Kenya Raila Odinga.