Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen China Hong Lei ya fadi yau Litini cewa Shugaban addinin nan na Tibet mai gudun hijira, Dalai Lama, shi ne ke ingiza masu kona kawunansu kurmus, kuma ana hakan ne don a tunzura mutane su shiga harkokin a-ware. Hong ya bayyana amfani da mutane don cimma wasu manufofi na siyasa da cewa ba abin amincewa ba ne.
Dalai Lama dai y ace bai goyon bayan duk wani tashin hankali.
Shugaban Sashin Kula da ‘Yancin dab adam na Majalisar Dinkin Duniya Navi Pillay ya yi kira ga hukumomin China ranar Jumma’a da ta magance korafe-korafen da Tibetawa su ka nuna sannan ta bar masu sa ido masu zaman kansu su kai ziyara a yankin.
Tibetawa da daman a zargin China da danne masu ‘yancin addini da al’ada, a daidai kuma lokacin da ‘yan kabilar Han na China masu rinjaye ke ta mamaye wuraren da ko bisa tarihi na Tibetawa ne. Tibetawa masu yawa sun kona kawunansu kurmus tun daga watan Maris na 2011 kuma da daman na bukatar Dalai Lama ya dawo. Gwamnatin Tibet da ke gudun hijira na da hedikwata ne a Dharamsala da ke Indiya.