Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zulum Ya Yi Allah-wadai Da Harin Boko Haram Da Ya Hallaka Manoma 40


Gwamnan Borno Babagana Zulum
Gwamnan Borno Babagana Zulum

Zulum ya jajantawa wadanda harin ya rutsa da su da iyalansu tare da ba da tabbacin cewar za a gano wadanda suka bata sannan a sake hadasu da iyalansu.

Gwamna Babagana Zulum ya Allah-wadai da harin da ‘yan ta’adda suka kai kan kauyen Dumba, dake kusa garin Baga na karamar hukumar Kukawa jihar Borno.

Gwamnan ya yi tir da harin da ya yi sanadiyar kisan akalla manoma da masunta 40 a Lahadin da ta gabata tare da yin kira ga dakarun aikin wanzar da zaman lafiya na “Operation Hadin Kai” da su bi sawu sannan su hallaka masu tada kayar bayan da suka addabi Dumba da sauran maboyarsu da ke yankin tafkin Chadi.

An ce mayakan kungiyoyin Boko Haram da ISWAP da ke gudanar da harkokinsu a yankin ne suka kai harin.

Zulum ya jajantawa wadanda harin ya rutsa da su da iyalansu tare da ba da tabbacin cewar za a gano wadanda suka bata sannan a sake hadasu da iyalansu.

Sanarwar da kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida na jihar, Usman Tar, ya fitar ta ruwaito gwamnan na cewa, “cikin alhini da bacin rai, na samu labarin harin da aka kai a Dumba inda ‘yan ta’adda suka hallaka dimbin manoma da masunta.

“A madadin gwamnati, ina jajantawa iyalan wadanda al’amarin ya rutsa dasu. Ina mai baiwa al’ummar Borno cewar za’a binciki wannan lamari yadda ya dace domin daukar mataki na gaba.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG