A yayin da shugaba Muhammadu Buhari, ke kokarin ziyartar jihohi uku dake kudancin tarayyar Najeriya, cikin wannan makon, an sami rarrabuwar kawuna dangane da wannan ziyarar duk kuwa da cewa ranar jumma’ar data gabata shugaban ya ayyana cewa ba da jimawa ba yankin zai fara amfana da ayyuka na gari da zasu taimaka gaya wajan bunkasa tattalin arzikin kasa baki daya.
Mr Ogochukwu Ogbonnaya, malami a wata jami’a dake yankin ya bayyana cewa zuwan shugaba Buhari yankin nada kyau domin ya ganewa idanunsa irin halin da jama’ar yankin suke ciki, kamar lalatattun hanyoyi, da karancin wutar lantarki koda shike bazai sami damar lekawa kasuwanni ba, zai gane cewa jama’a na cikin akuba, kuma matasa na zaman kashe wanndo.
Malam Adamu simple Man, dan arewacin kasar ne dake zama a daya daga cikin jihohin da shugaba Buhari zai ziyarta, ya kuma bayyana farin cikin sa musamman ganin yadda wannan ziyara zata kara dankon zuminci tsakanin kabilun.
Sai dai Malam Abdullahi Baban Hadiza Rigasa, a nasa ra’ayin bai ga alfanun wannan ziyara da shugaba Mohammadu Buhari, zai kai kudancin kasar ba, domin a cewarsa, ziyara ce da ya kamata a ce tun ba yanzu ba shugaban ya kai sai da ya fahimta cewa rigima na nema ta taso a lokacin mulkin sa.
Wannan shine karo na farko da shugaba Mohammadu Buhari zai ziyarci wadannan jihohi tun lokacin kama mulkinsa.
Daga Owerri ga rahoton da Alphonsus Okoroigwe ya aiko mana.
Facebook Forum