Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Ce Ba Gudu Ba Ja Da Baya


Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari, na Najeriya, ya kara jaddada kokarin da Gwamnati keyi da irin nasarorin da yake samu wurin yaki da cin hanci da rashawa da sha’anin tsaro.

Shugaba Muhammadu Buhari, yace Gwamnatinsa na samun nasara wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma tsaro a Najeriya.

Ya jaddada hakane a lokacin da yake ganawa da shuwagabanin addinai na Najeriya, yana mai cewa gwamnati ta kara dukufa wurin tabbatar da cewa wannan yaki ya kai kowane bangare na Najeriya.

Ya kara da cewa wannan yaki da gwamnatin tasa a gaba ba gudu ba ja da baya za a kara dukufa wurin inganta bangaren shara’a dana jami’an tsaro domin tabbatar da cewa an hada kai da shugabanin addinai wurin samun nasarar wannan yaki.

Da yake tsokaci akan ganawar da shugaba Buhari yayi da shuwagabanin addinai Pastor, Musa Dikwa, yace akwai mahimmanci a ganawar amma akwai damuwar a cewarsa domin wasu shugabanin addinai suma suna da badakalar cin hanci da rashawa domin yace shi kansa ya kai wasu shuwagabanin kara EFCC.

Ya kara da cewa zai yi wuya su maramasa baya domin wasu daga cikin shuwagabaini addanai suma akwai hannun su dumu dumu a batun cin hanci da rashawa a matakai daban daban.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:40 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG