Farfesa Adamu Baikie shi ne shugaban sabuwar kungiyar wanda ya ce an kafa kungiyar ne da nufin ganin an hada duk kawunan kiristocin arewa domin su yi magana da murya daya.
Farfesa Baikie ya janyo hankalin kiristoci da cewa ba’a kafa kungiyar saboda tsokanar fada ba, kuma ba’a kafa ta saboda neman wani alfarma ba. Injishi an kafa kungiyar ne saboda hadin kai da kuma kare mutuncinsu. Daga lokacin da aka kafa kungiyar zasu yi magana da murya daya.
Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Janar Yakubu Gowon mai ritaya shi ya shugabanci taron. Y ace fatarsa it ace samun hadin kai tsakanin mijami’u da kuma da dariku daban daban na kiristoci a arewacin Najeriya.
Mabiya addinin Kirista da suka fito daga jihohi daban sun bayyana ra’ayinsu akan sabuwar kungiyar. Iliya Ahmadu daga jihar Kano yayi farin ciki da kafa kungiyar. Haka ma wadanda suka fito daga jihohin Bauchi da Gombe suka jaddada.
Taron ya samu halartar manyan Kiristoci ‘yan arewa da suka hada da Kakakin Majlisar Wakilan Najeriya Yakubu Dogara da Janar T.Y. Danjuma mai ritaya da dai sauransu.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani
Facebook Forum