Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Yan Sandan Bauchi ta Kama Yan Fashi 42


IBRAHIM K. IDRIS, babban sifeton 'yansandan Najeriya
IBRAHIM K. IDRIS, babban sifeton 'yansandan Najeriya

Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta gabatar da wasu mutane wa manema labarai su guda arba’in da biyu wadanda ake zargi da aikata laifuka da dama a helkwatan yan jihar a Bauchi. Ana tuhumar su ne da laifuka kamar satar mutane don neman kudin fansa, fashi da makamai da sauransu.

Kakakin yan sandan jihar Bauchi DSP Kamal Datti da ya yi jawabi a taron manema labaran yace galibin wadanda suka kama yan wata kungiya ce mai kashe mutane babu hujja da ake kiranta Babeli kuma yan sanda sun kwace makamai masu tarin yawa da suke fashi da su.

Kakakin yan sandan Kamal Dattai yace sun yi wannan gagarumin nasarar kama miyagun ne saboda irin hadin kai da mutanen jihar Bauchi suke baiwa yan sanda. Ya kara da cewa duk wani mai aikata laifi ya san cewar komin dadewa yan sanda zasu kama shi.

Wasu yan fashi da makamin sun hira da wakilinmu Abdulwahab Mohammed kuma sun nuna masa yanda aka kama su. Tuni yan sanda suka shirya gabatar da masu laifin gaban shari’a.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG