Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun ECOWAS Ta Samu Najeriya Da Laifi Kan Zanga Zangar End SARS Na Shekarar 2021


ECOWAS
ECOWAS

Wata kotun yanki a Afrika ta yanke hukuncin cewa, hukumomin Najeriya sun take hakkin masu zanga zanga, a yayin gagarumar zanga zangar kin jinin cin zalin da yan sanda keyi, a shekarar 2020.

Zanga zangar da aka yi wa lakabi da End SARS, inda aka yi kiran rushe rundunar musamman ta yakar fashi da makami sakamakon zarge zargen azabtarwa, karbar kudi a hannun jama’a da kisan zalunci.

Kotun mai nasaba da kungiyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma, ko ECOWAS, ta fitar da hukunci a ranar Laraba, inda ta zargi hukumomin Najeriya da yin amfani da karfi ta inda bai dace ba a yadda ta maida martani ga zanga zangar, kusan shekaru hudu da suka wuce.

Hukuncin na kotun ECOWAS ya biyo bayan karar da hadakar masu fafutukar kare hakkin dan adam da wasu kungiyoyi a karshen shekarar 2021, shekara daya bayan gagarumar zanga zangar da ta nemi hukumomi su rushe bangaren musamman na rundunar 'yan sandan Najeriya, ko SARS. An dai zargi SARS din da azabtar da jama’a, amshe mu su kudi da kashe kashen zalunci.

Wadanda su ka shigar da karar, Obiamuju Udeh, Perpetual Kamsi, da Dabiraoluwa Adeyinka, sunyi zargin cewa, jami’an gwamnati sun yi mummunan keta hakkin dan’adam a rawar da su ka taka a yayin kwantar da zanga zangar a kan tituna.

Alkalai uku da su ka saurari karar a kotun, sun yanke hukuncin cewa, gwamnatin Najeriya ta yi amfani da karfin da ya wuce kima a yadda ta maida martani ga zanga zangar.

Kotun tace, ma su karar sun dandana azaba a hannun jami’an tsaron da suka keta hakkin dan’adam da kasashen Afrika su ka amince da su, da wasu dokoki da dama na kare hakkin dan’adam na duniya.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG