Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Gini Ya Rufta Da Daliban Sakandare a Jos


Yadda makarantar Saint Academy ta rufa a Jos (Hoto: Facebook/Gist With Blinky)
Yadda makarantar Saint Academy ta rufa a Jos (Hoto: Facebook/Gist With Blinky)

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na rana a unguwar Busa Buji da ke karamar hukumar Jos ta Arewa.

Rahotanni daga Jos a jihar Filaton Najeriya na cewa wani bene mai hawa biyu da ke dauke da makarantar sakandare ta Saint Academy ya rushe.

Kafofin yada labaran kasar sun ce wani sashen ginin ya rufta da dalibai da dama yayin da suke rubuta jarabawa.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na rana a unguwar Busa Buji da ke karamar hukumar Jos ta Arewa.

Bayanai sun yi nuni da cewa ma’aikatan agaji da na tsaro sun dunguma zuwa unguwar don kai dauki.

Wani hoton bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, wanda Muryar Amurka ba ta tabbatar da sahihancinsa ba ya nuna iyayen daliban suna ta kuka tare da neman a kai musu dauki.

Babu bayanai kan adadin daliban da ke cikin makarantar ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ko adadin wadanda suka mutu.

Rushewar gidaje, matsala ce da ta kusa zama ruwan dare a Najeriya musamman a jihar Legas da ke kudu maso yammacin kasar.

Kungiyar masu kare hadurran rushewar gidaje ta Najeriya ta ce a shekarar 2022, mutum 84 ne suka mutu sanadiyyar rushewar gidaje 62 yayin da mutum 113 suka jikkata.

Ashirin daga cikin wannan adadi na ruftarwar giaje a Legas suka faru a cewar kungiyar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG