Jamiyar CDS Rahama ta jamhuriyar Nijer, tana zargin shugaban jamiyar PNA Al'oumma, Alhaji Sanoussi Tambari Jakou kuma mashawarci na masamman na shugaban kasa da yin wasu kalamai mafi muni a cikin tarihin Nijer, inji jamiyar ta CDS Rahama.
A cewar kakakin jamiyar ta CDS Rahama, Alhaji Doudou Rahama, Tambari Jakou ya zargi shuwagabannin jamiyar CDS Rahama da kafa jam'iyyar da wata manufa da akida irin ta bukasa kabilanci da bambancin jinsi inji shi.
A Nijer ambaton kalamai na kabilanci ko bambancin jinsi na cikin manya-manyan laifuffukan da kundin tsarin mulki kasar ke kyama.
Dokokin kasar sun tanaji hukunci mai tsanani ga duk wadanda aka kama da wannan mummunan laifi .