Shugaban APC reshen jihar Borno Ali Bukar Dalori ya bayyana tsohon gwamnan a matsayin dan kawalcin PDP sabili da canza shekarsa zuwa PDP din.
Yace canza shekar da Ali Modu Sheriff yayi babu abun da zata ragewa APC a jihar Borno. Da Modu Sheriff zai yi tunani da nazari yau a ce ya bar APC abun mamaki ne kuma abun kunya ne. An zabeshi gwamna sau biyu an kuma zabeshi zuwa majalisar dattawa sau biyu. Tare da shi aka yi shirin gamayyar jam'iyyu da suka hade suka haifi APC.
Dangane da cewa Ali Modu Sheriff zai bar APC tare da 'yan majalisa su ashirin da biyar, Bukar Dalori ya karyata maganar. Yace shi kansa yana majalisar kuma duk 'yanuwansa basu da alaka da Ali Modu Sheriff.
Da aka tambayeshi dalilin da yasa ba zasu zauna su sasanta Ali Modu Sheriff da gwamna mai ci yanzu ba sai Bukar Dalori yace sun sha zama su yi hakan. Har kwamiti na mutum uku da aka kafa bai yiwu ba. Gaskiya ne Ali Modu Sheriff ya kawo gwamnan amma jama'ar Borno ta zabeshi. Sabili da haka basu da wani fargaba kuma ba zasu ja da baya ba domin Ali Modu Sheriff ya fice.
Batun cewa dama can Ali Modu Sheriff yana yiwa PDP aiki ya tabbata.
Kawo yanzu dai Ali Modu Sheriff ya gana da magoya bayansa inda ya shaida masu shirin ficewa daga APC. Yace zasu yi bikin gangamin shiga PDP bayan azumi.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.