Sai dai yace za sanya bangarori masu zaman kansu wajen gyagyara da kuma gudanar da matatun man fetur din.
Ga dai abinda ministan ke cewa.
‘’Zamu kawo abokan hulda da zasu zuba jari na kudi wurin gyara su da kuma gudanar dasu kana daga bisani in tafi mu zauna da shugaban kasa muga ko ya dace ayi batun sayar dasu amma dai har yanzu bamu samu amincewar shugabankasa na a sayar dasu ba, bana tsammani za a sayar da matatun man fetur din ba’’
Sai dai a waje daya kuma tsohon ministan man Fetur Alhaji Umaru Dembo yace ayi taka tsantsan.Shima ga abinda yake cewa
‘’Shaanin mai abu ne mai wuya musammam ma a kasa irin namu da wasu sukan danyi tawaye sun wahalar da kasar baki daya, musammam kasa irin tamu ta Najeriya ka mika hidimar man ka ga wau masu son kudi to hatta gwamnatin ma sai su durkusad da ita.Ni nafi son idan da hali su su kawo nasu matatan amma ba a basu na kasa su sarrafa shi ba’’.
‘’Ga Hassan Maina Kaina da Karin bayyani’’