Amurka da Japan da kuma Koriya ta Kudu, sune suka bukaci da a yi wannan zaman gaggawan da tsakar rana yau agogon gabashin Amurka.
Jiya lahadi ne kasar Koriya ta Arewa ta harba wannan makami mai linzami, wanda jami'an kasar Koriya ta Kudu suka ce yayi tafiyar kimanin kilomita 500 kafin ya sauka a cikin tekun Japan.
A Koriya ta Arewa, kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar, KCNA, yayi murnar gwajin abinda ya kira "wani sabon nau'in makami na Koriya" tare da ikirarin cewa shugaba Kim Jong Un da kansa ya sa ido wajen gwajin.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen China, Geng Shuang, ya fada yau litinin cewa kasarsu tana adawa da harba wannan makami mai linzami, abinda ya saba da kudurorin majalisar dinkin duniya. Ya kara da cewa kasar China, daya daga cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a Kwamitin Sulhun MDD, tana kira ga dukkan bangarorin da su kai zuciya nesa, su guji duk matakan tsokana. Yace China ta yi imanin cewa za a iya warware wannan lamarin ne kawai ta hanyar tattaunawa.
Ita ma ma'aikatar harkokin wajen Rasha a yau litinin ta bayyana damuwa game da harba wannan makami mai linzami.