Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga Zangar Nuna Fushi Ga 'Yan Sanda Bayan Harbe Wani Bakar Fata


Dimbin mutane sun sake wani sabon sintiri akan titunan birnin Charlotte a jihar Carolina ta Arewa dake nan Amurka a dare na biyu jere a jiya Laraba don bayyana jin haushinsu akan wani sabon harbi da yan sanda suka yiwa wani Ba’Amurke Bakar Fata.

Sun yi macin nasu na jiya Laraba cikin lumana ba kamar na shekaranjiya Talata ba wanda akayi rigingimu a cikinsa har aka kai ga raunata mutane kimanin 24 ciki har da yan sanda 16. Haka kuma Masu zanga zangar sun yi ta jifar yan sanda da duwatsu, suka tare wata babbar hanya kuma suka kona motar daukar kaya.

Hakan ya tilastawa yan sanda suka tarwatsa taron jama’ar da hayaki mai sa hawaye.

Shugaba Barrack Obama ya yi hirar waya da magajiyar garin birnin na Charlotte Jennifer Roberts da kuma Magajin Garin birnin Tulsa na jihar Oklahoma, Dewey Bartlett inda wani farar fatar dan sanda ya harbe wani mutum bakar fata har lahira a Juma’a da ta gabata da ya janyo zanga-zanga a garin.

Wani dan sanda Bakar Fata na birnin Charlotte ne dai ya bindige wannan bakar fatan mai suna Keith Lamont Scott dan shekara 43 da haifuwa, kuma ya kashe shi a ranar Talata a yayinda da shi da sauran yan sanda suke kokarin kawo wata takardar sammacin a gidan da mutumen yake.

Shugaban yan sandar yankin Kerr Putney yace yan sanda sun ga Scott ya sauko a cikin wata mota dauke da bindiga kuma yaki sauraren umurnin da suke bashi da kakkarfar murya na cewa ya ajiye makamin.

To sai dai Iyalan Scott sun musunta wannan batu suka ce babu makami a hannunsa, yana dauke da wani littafe ne kawai, yana jiran motar makaranta ta sauke dan sa dake ciinta. Wasu da suka shaida wannan abu sunce ya gada hannayensa sama amma sai daya daga cikin yan sandar ya bude wuta a kansa.

Amma shugaban na ‘yan sanda yace bindiga suka gani kusa da Scott amma ba littafi ba.

XS
SM
MD
LG