Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Masu COVID-19 Ya Doshi Miliyan 29 a Duniya


Wani ma'akacin lafita sanye da rigar kariya daga cutar COVID-19 a Indonesia, Laraba, Satumba. 9, 2020
Wani ma'akacin lafita sanye da rigar kariya daga cutar COVID-19 a Indonesia, Laraba, Satumba. 9, 2020

Jimullar wadanda cutar Coronavirus ta kama a sassan duniya na ci gaba da karuwa yayin da har yanzu Amurka, India da Brazil suka kasance kasashen da cutar ta fi kamari.

Rahotannin na nuni da cewa, adadin wadanda cutar COVID-19 ta harba a duk fadin ya kuso kai wa miliyan 29.

Amurka ce dai kasar da ta fi kowace yawan wadanda suka kamu da cutar inda take da same da mutum miliyan 6.4.

India wacce ke a matsayi na biyu, ta wuce Brazil, inda take da yawan mutum miliyan 4.7.

A yau Lahadi alkaluma sun nuna cewa adadin wadanda suka kamu da cutar a jihar Maharashtra da cibiyar hadahadar kasuwancin ta Mumbai ke cikinta, ya haura miliyan daya.

Hakan kuma ya haifar da cikas ga matakan da hukumomi ke dauka don farfado da tattalin arzikin kasar.

Ita dai Brazil tana da mutum miliyan 4.3 na wadanda cutar ta harba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG