A yayin da China ta ke ikirarin kai karshe a samar da rigakafin cutar coronavirus, Beijin ta soma yin alkawarin samar da rigakafin cigin gaggawa ga wasu kasashe na musamman.
Ana ganin wannan kokarin a zaman wata hanya da Beijin ke kokarin amfani da ita wajen daukaka matsayinta a duniya, bayan barkewar annobar da ta soma daga birnin Wuhan ta kuma yadu a sauran sassan duniya.
Kasashe da dama da ke yankin kudancin tekun China, na cikin yankunan da Beijin ta ke kokarin yada gangamin difilomasiyyarta na rigakafin.
A cikin watan Yuli, Ministan Lamurran Cikin Gida na China ya yi wa kasar Philippines alkawarin ba ta fifiko wajen samar da rigakafin. A watan Agusta kuma wani babban kamfanin hada magunguna na China ya rattaba hannun yarjejeniya da kamfanin hada magunguna mallakar gwamnatin kasar Indonesia mai suna PT Bio Farma, domin samar wa Jakarta rigakafin har miliyan 250 kowace shekara.
A farkon watan Satumba, wani dan majalisar dokokin China Yang Jeichi, ya ziyarci Myanmar, ya kuma yi alkawarin cewa Beijin za ta ba da kulawa sosai ga Yangon ida har ta sami rigakafin.
Facebook Forum