Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga Zangar Birtaniya: Najeriya Ta Shawarci 'Yan Kasarta Su Yi Taka-Tsan-Tsan


Zanga Zanga a Bristol, August 3, 2024.
Zanga Zanga a Bristol, August 3, 2024.

An shiga zaman dar-dar sakamakon yadda zanga-zangar da aka danganta da ta masu tsatsauran ra’ayi ke ci gaba da bazuwa a sassan kasar Britaniya, biyo bayan kisan wasu yara mata uku da aka yi a wani gidan rawa.

Kawo yanzu dai zanga-zangar ta ci gaba da bazuwa a biranen Britaniyan inda aka yi ta ganin yadda masu boren ke kone-kone suna balle shagunan a yayin da jami’an ‘yan sanda suka yi ta harba hayaki mai saka kwalla domin kwantar da tarzomar

Dakta Salim Abatcha dan Najeriya mazaunin birnin Manchester inda rikicin ya fi kamari ya ce shakka babu ana fuskantar barazana daga masu kyamar baki amma gwamnati na daukar matakin da ya dace

A dai farkon wannan makon ne, wasu masu ra’ayin rikau suka shirya zanga-zangar bisa zargin baki da hannu a kisan wasu yara mata uku a wani gidan rawa da ke yankin Southport, bakin suma dai sun shirya tasu zanga-zangar don nuna adawa da zanga-zangar kyamar baki, a lokuta da dama sai jami’an yan sanda sun yi da gaske don hana arangama a tsakanin bangarorin biyu

Furanni da aka ajiye domin jimamin mutuwar wadansu 'yan mata uku
Furanni da aka ajiye domin jimamin mutuwar wadansu 'yan mata uku

Kasashe kamar Najeriya da Malaysiya da Indonesiya da Hadaddiya Daular Larabawa sun gargadi al‘umominsu da su yi taka tsantsana a kasar a yayin da gwamnatin Australiya ke cewa zanga-zangar ta bude kafar aukuwar ayyukan ta’addanci…..Idowu Olayinka dan Najeriya ne da y ace, gargadin da gwamnatin Najeriyar ta yi yasa ya kara daukar matakin ganin rikicin bai ritsa da shi ba…y ace duk da cewa rikicin bai kai inda yake ba amma tuni ya kara daukar matakin kariya tun bayan da ya ji sanarwar gwamnatin Najeriyar ina dai kallo a talabijin yadda ake ta kone-konen motoci da shaguna..

Tuni dai Firaiminista Keir Starmer ya yi ma yan kasar jawabi yana mai cewa ko kadan gwamnatinsa ba za ta laminci duk wani yunkuri na haddasa kiyaya a kasar ba.

Saurari cikakken rahoton Ramatu Garba:

Zanga Zangar Birtaniya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG