Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Wakilan Iran Suna Kiran A Rataye Shugabannin 'Yan Hamayyar Kasar


A wan nan hoto ana ganin masu zanga zanga suna jifar 'yan sandan kwantarda tarzoma.
A wan nan hoto ana ganin masu zanga zanga suna jifar 'yan sandan kwantarda tarzoma.

Kwana daya bayan muhimmin zanga zanga kan titunan Farisa tun bayan bore da aka yi a kasar a 2009,wakilan majalisar dokokin Iran suna kiran a hukunta shugabannin ‘yan hamayyar kasar kuma a rataye su.

Kwana daya bayan muhimmin zanga zanga kan titunan Farisa tun bayan bore da aka yi a kasar a 2009,wakilan majalisar dokokin Iran suna kiran a hukunta shugabannin ‘yan hamayyar kasar kuma a rataye su.

Wakilan majalisa masu ra’ayin rikau sun gudanar da zanga zanga a majalisar dokokin kasar jiya Talata,suna cika suna batsewa,suna kira da hukumomi su rataye Mir Hossein Mousavi, da Mehdi Karroubi,saboda tada zaune tsaye,tuni 'yan hamayyar biyu suke ake musu daurin talala cikin gidajensu tun makon jiya.

Fiyeda wakilan majalisa 220 suka fidda sanarwar neman a gurfunadda shugabannin ‘yan hamayya kan zargin cin amanar kasa,laifi da yake dauke da hukuncin kisa.

Wani limami Ahmed Khatami,nadin shugaban malaman Iran Ayatollahi Ali Khameni shima ya tsoma bakinsa,yana zargin ‘yan hamayyan da laifin yakar addini,da aka yi wa tanadin hukuncin kisa a Iran. Shi dai Moussavi da Karroubi sun kira da a yi zanga zangar ranar litinin,domin bayyana goyon baya ga al’umar Masar da Tunisia.

Wadan nan kiraye kiraye sun saka shugaban malaman Iran cikin tsaka mai wuya,domin shine kotun karshe kan dukkan wasu muhimman batutuwan kasa.

Ahalin yanzu kuma,shugaban Amurka Barack Obama,ya yi Allah wadai da fatattakar masu zanga zanga nuna kyamar gwamnati a Iran,wadanda boren ‘yan Masar ya tsuma,daga nan ya yi kira ga dukkan gwamnatoci a duk fadin gabas ta tsakiya su kasa kunne kan bukatun al’umarsu.

XS
SM
MD
LG