Shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh ya bada sanarwar jerin matakan sassauci da suka hada da shirin gwamnatinsa na aiwatar da sauye sauyen cikin tsarin mulkinn kasar da ada zai bashi damar mulki har iya rayuwarsa,ya kuma yi alkawrin dansa ba zai gajeshi ba.
Shugaba Saleh wanda ya yi shekaru 32 yana mulki jiya laraba ya bada sanar cewa babu Karin wa’adi,babu magajinsa,kuma ba za’a sake lale bayan an kama hanya ba. Yana magana ne kan kdurin jam’iyya mai mulkin kasar na bullo da kayyade wa’adi,d a ake ganin wani shiri na shugaban ya sake yin takara.
Shugaban da ya juma yana mulki,kuma kawan Amurka ne a yaki d aal-Qaida, ya gayawa majalisar dokokin Yemen cewa ba zai yi kokarin tazarce ba idan wa’adin mulkinsa na yanzu yak are a 2013. Mr. Salhe ya yi jawabi ne ga majalisar dokokin kasar,amma ‘yan hamayya wadanda galibi aka ce masu bin tafarkin addini ne sun kauracewa masa.
Kamfanin dillancin labaran Yemen da ake kira SABA ya bada labarin shugaba Amurka Barack Obama ya kira takwaran aikinsa na Yemen din domin ya bayyana goyon bayansa ga matakai da shugaban ya fara dauka.
Sanarwar da shugaban ya bayar yazo ne kwana daya gabanin wani gangamin da ‘yan hamayya suka shirya yau Alhamis, da suka lakabawa sunan “ranar kulewa”,dazai kasance ci gaba da kananan zanga zanga da jerin gwano da ‘yan gwagwarmaya sukace ya samo asali daga borin ‘yan Tunisia da Masar. A jawabinsa na jiya Alhamis shugaba Saleh ya yi kira da dakatar da dukwani shirin zanga zanga.