Mahukunta a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya sun bayyana kafa dokar hana fita tsawon sa’o’i 24 a karamar hukumar mulkin Katagum, sakamakon tarzomar da ta barke yayin zanga-zangar nuna kin jinin matsin rayuwa da ke gudana a duk fadin kasar.
Rahotanni sun bayyana cewa daruruwan matasa ne suka fantsama kan titunan karamar hukumar suna zanga-zanga, inda daga bisani kuma ta rikide zuwa kone-kone da fashe-fashen kayayyakin gwamnati da na daidaikun jama’a.
Matasan sun kai farmaki kan sakatariyar karamar hukumar tare da cinnawa wani sashen ofisoshi da wasu motoci wuta da kuma wawushe kayayyaki. Haka kuma sun kai hari tare da lalata gidan tsohon mataimakin gwamnan jihar Alhaji Baba Tela.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Awwal Musa Muhammad ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Yace “mutane sun fito zanga-zangar da yawan gaske, sai kuma suka fara lalata kayan jama’a kamar Sakatariyar karamar hukuma, inda suka cinna mata wuta, amma Allah ya taimakemu ba su kona ta gaba daya ba.”
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce sun kuma kai hari a gidan gwamnatin jihar da ke Azare, inda suka soma ciccire kayayyaki, kafin jami’an tsaro su tarwatsa su, tare kuma da kwace wasu kayayyakin da suka soma wawushewa.
“Wannan ya sa muka gudanar da taron gaggawa na tsaro inda mu ka ga cewa wannan abu idan aka bar shi zai iya tabarbarewa. Kan haka ne aka kafa dokar hana fita sa’o’i 24, domin baiwa jami’an tsaro damar dawo da kwanciyar hankali a yankin” in ji kwamishinan ‘yan sanda Awwal Musa.
Wasu mazauna Azare da wakilinmu ya zanta da su sun tabbatar da ganin mutane 3 da suka sami raunin harbin bindiga a yayin arangama da jami’an tsaro, haka kuma sun tabbatar da daga tutocin kasar Rasha a lokacin zanga-zangar.
Gwamnan jihar Bauchin Bala Muhammad, ya yi Allah wadai da tashin hankalin, duk kuwa da cewa ya nuna goyon baya ga matasan jihar masu zanga-zangar.
Gwamnan ya ce jawabin shugaban kasa kan zanga-zangar na daya daga cikin abubuwan da suka kara harzuka jama’a, kasancewar “jawabin duk fanko ne da sam bai ma fuskanci batutuwan da masu zanga-zangar suke korafi a kai ba,” a ta bakin gwamnan na Bauchi.
Saurari rahoton Abdulwahab Muhammad:
Dandalin Mu Tattauna