Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Sa Kafar Wando Daya Da Masu Kiran A Yi Juyin Mulki A Najeriya - 'Yan sanda


Shugaban 'yan sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun (Hoto: Facebook/Rundunar 'yan sandan Najeriya)
Shugaban 'yan sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun (Hoto: Facebook/Rundunar 'yan sandan Najeriya)

“'Yan sandan Najeriya na yin gargadi da kakkausar murya ga wadanda suke daga tutar wata kasa da yin kira a yi juyin mulki." In ji rundunar 'yan sandan kasar.

Hedkwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta gargadi masu kiraye-kirayen sojoji su karbi mulki a kasar.

Rahotanni da dama sun ruwaito yadda wasu masu zanga-zanga suke kira ga dakarun kasar su karbi mulki daga hannun gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Wasu daga cikin masu boren har ila yau sun yi ta daga tutar kasar Rasha domin jan hankulan hukumomi.

Tun daga ranar 1 ga watan Agusta masu zang-zangar suka bazama kan tinunan wasu biranen kasar suna nuna korafi kan matsalar tsadar rayuwa da ta dabaibaye kasar.

Sai dai a wata sanarwa ta fitar a ranar Talata dauke da sa hannun kakakinta ACP Olumuyiwa Adejobi, rundunar ta yi gargadi da kakkausar murya.

“’Yan sandan Najeriya na yin gargadi da kakkausar murya ga wadanda suke daga tutar wata kasa da yin kira a yi juyin mulki.

“Yin hakan cin amanar kasa ne karkashin tsarin dokar Najeriya.” Sanarwar ta ce.

Zanga zanga a jihohin Bauchi, Kano, Kaduna da Katsina sun jirkice sun koma tarzoma inda wasu bata-gari suka rika kai hari gine-ginen gwamnatin da wuraren ‘yan kasuwa.

“Bayyana tutar wata kasa da kira a yi juyin mulki babban laifi ne, ya kuma nuna ainihin aniyar wadanda suka shirya zanga-zangar ta kokarin hargitsa tsarin Dimokradiyya a Najeriya.” In ji ACP Adejobi.

Ko a ranar Litinin ma Babban hafsan tsaron Najeriya Janar Christoper Musa, ya yi gargadi ga masu daga tutar ta Rasha yana mai cewa za su dauki mataki akansu.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG