Yayinda a jamhuriyar Nijer ake shirin rantsar da sabon shugaban kasar Bazoum Mohamed, a ranar 2 ga watan Afrilu, wanda zai gaji shugaba Muhammad Issouhou mai barin gado, dan takarar jam’iyar adawa ta RDR Canji Mahaman Ousman, wanda ya sha kaye.
Ousman ya umurci magoya bayan nasa da su fara fita ne daga ranar Talata 30 ga watan Maris, har sai an mayar masa da nasarar da ya ce ya samu a zaben 21 ga watan Fabrairu. Sai dai magoya bayan jam’iyya mai mulki na cewa batun zabe ya wuce a wurinsu.
A wani taron manema labarai da ya kira a gidansa a karo na 2 cikin mako guda, Alhaji Mahaman Ousaman, ya sake jaddada matsayinsa na wanda ya lashe zaben da ya gabata, domin a cewarsa alkaluman da ya tattaro daga sassan kasar, sun tabbatar masa da cewa, shi ya sha kaye a fafatwarsu da Bazoum Mohamed.
Alhaji Mahaman Ousaman, ya ce ba zai yarda a yi masa kwacen kuri’u ba, dalilin da yasa ya umurci magoya bayansa da su fito kan tituna don gudanar da zanga zangar lumana.
A yanzu haka wasu mukarraban jam’iyun kawancen adawa irinsu tsohon Firai Minista Hama Amadou na can kulle a kurkuku, saboda zarginsu da hannu a tarzomar da aka fuskanta a birnin Yamai da Zinder a washegarin fitar da sakakmakon wucin gadi na zagaye na 2 na zaben shugaban kasar.
Dan takarar na ‘yan adawa ya bukaci a gaggauta sakin wadanan ’yan siyasa saboda a cewarsu an kama su ba tare da aikata laifin komai ba.
Da yake maida martani akan wadanan korafe korafe, kakakin jam’iyar PNDS mai mulki Alhaji Assouamana Mahamadou, ya danganta irin wannan kame da cewar kame ne na wanda ya rasa tudun dafawa. Yana mai cewa batun zabe wata magana ce da tuni aka bar ta a baya.
A ranar 2 ga watan Afrilu ne dai ake sa ran rantsar da Bazoum Mohamed don soma wa’adin mulki na shekaru 5, kamar yadda kundin tsarin mulki kasar ya tanadar.
Wani mai bada shawara a fadar shugaban kasar Nijar Sanoussi Tambari Jakou, a lokacin kaddamar da wata gidauniya da shugaba Issouhou Mahamadou, mai barin gado yayi, a karshen mako ya gargade shi da ya sallami dukkan fursunonin siyasar dake tsare a gidan yari. Domin a cewarsa yin hakan wani mataki ne da zai wanke shi daga dukkan wasu zarge zarge marassa tushe.
Saurari rahoton wakilin Muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma, cikin sauti.