Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zambar N6M: Kotu Ta Daure "Mama Boko Haram'' Da Wasu Mutane 2 Shekaru 15


Mama Boko Haram
Mama Boko Haram

Yayin zaman kotun, lauyoyin masu kara, Mukhtar Ahmad da Shamsudeen Saka sun gabatarwa kotun da shaidu 3 da dimbin takardu a matsayin hujjar hukumar EFCC a kan wadanda ake kara.

A Alhamis din data gabata, Mai Shari’a Aisha Kumaliya ta babbar kotun jihar Borno, dake birnin Maiduguri, ta samu Aisha Wakil da aka fi sani da Mama Boko Haram da wadansu mutane 2 da laifi tare da aikewa dasu zuwa gidan kaso tsawon shekaru 5 kowannensu.

Shugaban sashen yada labarai na hukumar EFCC, mai yaki da almundahana a Najeriya, Dele Oyewale ne ya bayyana hakan a jiya Litinin.

An gurfanar da Wakil wacce ta kasance babbar jami’ar gidauniyar bada agaji ta “Complete Care and Aid Foundation tare da manajan tsare-tsarenta, Tahiru Sa’idu da kuma babban daraktan gidauniyar a Najeriya, Yarima Lawal Shoyode a gaban kotu a jiya Litinin akan tuhume-tuhume 4 da aka yiwa kwaskwarima dake da nasaba da zambar Naira milyan 6 da bada bayanan karya.

Yayin zaman kotun, lauyoyin masu kara, Mukhtar Ahmad da Shamsudeen Saka sun gabatarwa kotun da shaidu 3 da dimbin takardu a matsayin hujjar hukumar EFCC a kan wadanda ake kara.

Bayan haka ne, Mai Shari’a Kumaliya, ta zartar da hukunci tare da aikewa da wadanda ake kara zuwa gidan gyaran hali tsaron shekaru biyar-biyar ba tare da zabin tara ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG