Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miliyoyin 'Yan Kasar Indiya Sun Yi Zabuka


Mutane dake kan layin kada kuri'a jiya a kasar Indiya
Mutane dake kan layin kada kuri'a jiya a kasar Indiya

Miliyoyin 'yan Indiya suka yi zabubbukan matakin na uku a cikin shirin dimokradiya da masana suka ambato shi ne mafi girma a duk fadin duniya

Jiya Alhamis miliyoyin yan kasar Indiya suka yi zabubbuka a mataki na uku, wadanda suke da muhimmanci ga begen babar jam'iyar masu hamaiya ta Hindu Nationalist BJP a takaice na kawo karshen mulkin shekaru goma na jam'iyar Congress.

Tarzoma ta barke a mazabu da dama jiya Alhamis.

Wani bam da ake zaton ya tawayen Maoist ne suka jefa ya kashe sojojin Indiya guda biyu da raunana akalla mutane uku a jihar Bihar dake gabashin kasar.

'Yan tawayen Maoist sunyi kira ga masu zabe da suka kauracewa jefa kuri'a, suka kuma yi barazanar cewa zasu dagula zaben.

Kusan yan Indiya miliyan dari da goma ne suka cancanci yin zaben na jiya Alhamis a mazabu a jihohin Indiya goma sha daya da kuma wasu yankunan taraiya guda uku.

Prime Ministan kasar bai barin gado, Manmohan Singh yace zai zama bala'i ga kasar Indiya, idan har jam'iyar BJP ta masu hamaiya ta samu nasarar kuma dan takarta Narendra Modi ya zama sabon Prime Minista.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG